Wednesday, February 9, 2011

Tsokaci akan Nasihar da Malan muhammad Ali Umar ya gabatar a masallacin abu Huraira da ke Polo club sokoto.

TARBIYA


Tarbiya zata iya daukar wasu ma’anoni da yawa. Da farko zamu iya bata ma’anar ALBARKA. Albarka a nan ba ana nufin yawaba amma idan muna son fahimtar ma’anar to sai mu buga misali da Kare da Tumaki. Zamu ga cewa Kare yana da yawan haihuwa ga kuma diyan a haifo su da yawa wani lokaci takwas takwas, bakwai bakwai , hudu hudu da dai sauran su. Sannan kuma ga taurin rai, zaka ga yana da wuyar mutuwa. Amma zamu ga duk wadanan abubuwan da ya dace ace, ya yadu bai sa yayi yawan Tumaki da Awaki ba .Duk da kuwa mun san yawan yanka su da ake yi domin ci a kullum. Amma saboda albarkar da ke gare su zaka ga koda yaushe suna nan garke-garke duk da kuwa hauhuwarsu iyakarsu biyu- biyu, daya- daya sai can kaga ukku.
A wani gefen kuma ana iya kasa Tarbiya gida ukku.
1.RENO: A reni yaro a dauko mataki har yakai inda ake son yakai.
2.Dawwama ba tare da yankewa ba tare da zare damtse ga reno ga yaron da yake tarbiyyanta. Tarbiyyar ta zama ta Ruhi,Zucciya da Jiki.
3.Shine za’a iya gyara wani abu daga cikin mutum har ya kai baya bukatar kula zai iya tsayuwa da kansa. A takaice bai da wani abu na alfasha da sauransu.
Malaman musulunci sun ce a shirya mutum akan aqida ta sanin Allah subhanahuwa ta ala, na sanin Ihsani da  sakamakon lahira da Sallah da azumi. Hakuri da tawakkali da gaskiya da amana da barin karya da zama da makaryata. A kula da abinci na halal da haram. Tsaftataccen abu ya zama yana shiga cikinsa,  idan ya dauko abu zai ci a nuna masa ya tsaftace shi, Idan ya’yan itacene kuma basu da tsafta to sai ace “wanke shi kafin kaci”. Idan zai ci abinci ace ka wanke hannunka idan ya kare ace ya wanke hannunsa. Watau dai a kula da lafiyarsa.

                     MUHIMMANCI TARBIYA


1.Samu da idar da amanar da Allah ya bashi. Hakika sai Allah ya tambayeki game da tarbiyar ya’yanka. Manzon Allah ya gaya muna kowa makiyayi ne kuma sai an tambaye shi da abin kiwonsa.
2. Wani abu ne na samun lada. Hadisi ya tabbata da cewa idan mutum ya mutu sadakatu jariya kawai zata amfane shi. Watau Ilmi mai amfani ga al’umma. Misali wanda idan ka mutu mutane zasu ci gaba da amfani dashi, kamar buga littafai, yin wani bincike ka gano wani abu da mutane zasu amfana da sauransa. Na biyu, Sadakatul Jariya, misali gina massallaci,makaranta ,rijiya da sauransu. Sai kuma Da na gari, idan yayi ma addu’ah ko wani aiki na alheri bayan ka mutu.

                KASHE- KASHEN TARBIYA


Mata suna tarbiyya kashi biyar;
1.Akan son rai, Idan tana jin dadi ta faranta mishi rai, idan ranta ya baci ta duke shi da sauransu. Babu hasken wahayi, watau bata tuna Allah da manzonsa lokacin yin hukunci.Sai dai ta biye zucciya. Mun kuwa san ance “Don rai ya baci, kada hankali ya bata”
2.Akan yadda aka tarbiyyanceta. Abinda ake hana ki,ki hana shi,abinda da aka bar ki kika yi, kice shima yayi koda ya saba ma addini.Wannan tarbiyar tana da matsala.
3.Yan gari suyi mishi tarbiya. Misali ,Abinda suka bar yaransu sukayi,kema ki bar naki,idan sukayi laifi aka barsu,kema ki ki hukunta naki.Kuma kada kiyi nawa wurin raba yaranki da yaran da basu da halayen kwarai koda rayuka zasu baci.
4.Koyi da kwaikwayo.
Misali ,Idan akayi ma wane,shima sai ayi mishi.Idan aka canza ma wane wani abu, shine lokacin za’a canza masa koda yaushe. Ya zama cewa ya sagarce da gasa.
5.Tarbiya akan Al-Qur’an da sunna ta Annabi [S.A.W].Wannan itace ya dace ayi amfani da ita. Itace tarbiyyar da zata tsirar da yaro.
 Kamar yadda Imam Suyyudi ya fada na cewa, yaro wani amana ne akan iyayensa zucciyarsa kamar sabon sisi ne na zinari da baya da wani zane. Duk zanen da aka yi masa zai dauka.
   Duk yadda uwa zata kare yaronta daga wutar duniya,to ta lahira ce mafi cancanta ta kareshi.Yana da kyau iyaye su gyara masa tarbiyyarsa da hana shi zama da miyagun abokai.

             NAU’O’I KO [POINTS] DIN

                         YIN TARBIYA

 
1.Abu ne mai wahala.Sanin cewa abu ne mai wahala zai sa ki shirya daukar wannan wahalar. Zaki ga yaran kala-kala ne ko wane da halinsa. Balle kice, na san yadda nake renon wane haka zanyi da wane, To zaki ga wani yafi hakuri wani yafi saukin lallashi da sauransu. Kuma ita Tarbiya abu ne da ke bukatar ci gaba, wannan ma na kara mata wahala.
2.Yaren da zaki yi aiki dashi a aikace yafi amfani da wanda zaki yi a fade. Ba koda yaushe zaki yi a fade ba wannan zai yi tasiri idan akwai fahimta a tsakaninku. Misali, idan daga lokacin sallah yayi kika mike kika yo alwala sannan sai kice  ‘mu fa je muyi Sallah lokaci yayi’’ to zai fi tasiri,akan kiyi ta fadin ku tashi ku yi Sallah, ke kuma kina sha’aninki.
3.Duniyarsa ta saba ma tamu. Ya zamanto kina bi ta hanyar lallashi ba ta tsiya ba. Manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam ya nuna ma Aisha cewa taushi yana sa abu kyau, a inda tsanani yake bata shi.
4. Ki koya masa gaskiya da amana. Karya abu ne mai wuyar bari. Ki koya mashi juriya da fadar gaskiya da neman gafarar Allah idan yayi laifi. Sa’annan ki koya masa dauriyya wurin yin Ibada da kuma sauran lamurransa na rayuwa. Misali kada kiyi sanyin tada shi Sallah musamman ta asuba komai sanyi, matukar ya kai shekarun koyon Sallah watau bakwai. Ki dabi’anci sa shi barchi da wuri domin ya huta kafin asuba. Ki sani idan ya balaga baya Salla har ya mutu, idan an je lahira za’a tambaye ki,watau kina da [commisio] idan har da ganga ki ka ki dinga koya masa Sallah wai ke kina tausansa ba ki son ya tashi akwai sanyi, ko kuma a’a kawai, kada ya ga kina matsa masa. ko kawai kina son sa, kada a hana shi kallo. Yana da kyau ki tarbiyyance shi da cewa idan kika fadi Magana musamman da ta shafi addini ko ta gaskiya, to ki daure ki tsayu a kanta. Haka zai jawo miki girma a wurinsa, yasan idan ana maganar Ibada ko karatu ko gaskiya, ko wani abu na alheri ba kya wasa.
5.Yaro yana son uwayensa ,yana ganin komai zai yi kina son sa. To kada ki tozarta shi, ki bata wannan tunanin. Ki kula da lafuzzanki a gabansa da sauransu. Idan yayi kure ki nuna mamaki, ki gyara masa kurensa. Misali kice ‘a’a kamar ka ke karya? abin da mamaki”. In shaa Allah idan kina bi da dubara zaki ga ya gyara.
6. Ki guji zaginsa ko wulakanta shi a gaban mutane.
7. Hanyarki ta wa’azi ta zama hanya ce ta (tambihi) watau dubara. Kada ki zage shi. Ki nuna masa abinda yayi watau (hali ko tabi’a) shine bai kamata ba,ba shi kanshi ba. Watau bashi ake ki ba, halin da yayi.
8. Kada ki fito mai da tufafin ke ba kya laifi. Watau idan kin yi ba dai dai ba, ki nuna laifinki da tuba a gaban shi. Ki rinka sake mashi fuska yadda zai gyara miki laifinki. Misali akwai wata kawata da ta gaya min cewa tana da exercise book mai hoto,da yaronta ya gani sai yace, “yaya aka barku Islamiyya kuna zuwa da littafi mai hoto?” Sai yaje ya samo cover marar hoton mutun ya cire waccan ya sa mata marar hoton. kun ga zamu ga cewa wannan yaro in shaa Allah ya samu kyakkyawar tarbiyyar musulunci domin ko tarihi ya nuna da aka ci Makka manzon Allah sallahu alihi wa sallam ya umurci a goge hotunan da ke cikin Kaaba tare da karya gumakan da ke ciki.Watau shi hoto idan bada lalurar passport ba ko karatu ko sauran lalurorin da shari’a ta yarda dasu ba’a sonsa. [Karin bayanin mai tsokaci] .Ki rinka nuna mashi tsoron Allah ne mafi muhimmanci.Yadda ko baki nan yasan cewa Allah yana nan kuma Shine yafi dacewa aji tsoronSa. Da ke dashi duka kuna tsoron Allah kadai. Ko baki nan Allah yana ganinsa.
8,Adalci a tsakanin Ya’ya. Idan kina rashin adalci zai sa suki junan su. Idan kin tashi sayen abu ko kyauta ba babba ba karami duk kiyi musu dai dai.
9.Daidaita tsanani da sauki. Idan yayi abin kwarai kiyi masa kyauta. Yaro idan shekarunsa ba suyi goma ba, ba’a dukansa, Idan ma za’a yi to kada a doki fuska da kai. Haka ma bulala itama kada ta wuce goma. Misali idan laifin ya tsananta,sai ki jashi gefe kice kawo hannunka,kiyi masa kilan bulala biyu kice idan ka sake biyar zanyi maka. Kada ki manta idan ya sake ki cika alkawalin, tare da nuna masa munin abin. kuma kada ki tona masa asiri.
10.Yin fada lokacin da ya dace. Kada ki ga ya dace ki bashi shawara ko ki tsawata,sai kawai ki share ki yi kamar baki gani ba. Duk da kuwa ance idan yaro yayi laifi ya dinga boyewa, yana da kyau ki kyale  shi, idan kin lura  ya tuba. Amma idan ya sake, sai ki jashi gefe ki nuna masa illar sa kina gargadinsa  da tsoron Allah da illar kada mutane su sani zai kunya ta. Idan ya sake sai ki yi masa hukuncin da ya dace a lokacin. [Karin bayanin mai tsokaci].Allah yasa mu dace.
Daga baya anyi bayanin ba laifi a samu wata tatsuniya ko labari dake nuni da halaye na kirki ana gaya ma yara domin su kara fahimtar tabi’un kwarai da sakamakonsu da kuma kara dubarun zaman duniya.[Ba’a ce film ba].

MISALI

LABARIN WASIYYA WANI  MUTUM GA DAN SA.

Wani mutum yana ciwon ajali sai yace ma dansa idan ya rasu yaje wurin Tururuwa da Kare da Tsohon Doki suyi masa wasiyya. [To kun ga mun san wadannan abubuwa basu Magana amma gashi an buga misali da cewa zasu yi wasiyya].
Da yaje wurin Tururuwa, sai taje dashi wani daki inda aka ajiye wani buhun gero.Tace masa “kaga zan iya daukar buhun nan ni kadai?” yace “a’a”. sai taje ta nemo yan uwanta suka fara dibar hatsi guda- guda wani ma idan yayi girma a raba biyu ,da haka har suka kwashe duka. Sai tace kaga amfanin taron dangi, abu komai wahalar sa idan kuka hada kai da yan uwanka sai ku ci nasara in shaa Allah. Daga nan sai yaje wurin tsohon doki, shi kuma ya same shi daure duk yayi kashi ya bata turkensa, sai yace masa kaga da duk inda sarki zai je dani yake zuwa ayi min kawa,amma yanzu kaga ko kashi na ba’a kwashewa, da wani na ake yi. Saboda haka idan kana cikin kurciyyarka kayi abinda ya dace kuma zai amfaneka[misali aure,karatu da sauransu] domin idan lokacin ya wuce shikenan,[sai ka roki Allah ya taimakeka]Allah yasa mu dace.
Daga karshe sai ya nemi kare shi kuma. Sai yace “muje ka gani”. Suka kama hanya sai makaranta, yara na ganinsa suka taso da kuwwa suka kore shi, bayan sun bar nan sai yace suje wurin mafarauta,suna isa aka fara kiransa ana shafarsa. Sai yace to ka gani,nan ne bana so amma nan ake sona, saboda haka koda yaushe kaje wurin da ake sonka, ba inda kai kake so ba.

LABARIN ABOKIN SHAIDAN

Wani mutum ne kullum idan ana hira, idan yaji an zagi shaidan sai yace, shi dai tun da kowa zagin shaidan yake yi to shi, shi ne abokinsa. Ana nan wata rana sai yayi mafarkin shaidan,sai yace masa aboki zo muje yawo, ya goya shi a bayansa suka tashi sama. Suna cikin tafiya sai mutumen ya ji fitsari yace ,“Aboki ka dan sauka kasa ina son zanyi fitsari”. Sai shi kuma yace “haba aiba komai yi abinka kawai”, sai mutumen yace “haba, yaya zan yi ma fitsari a baya?” shaidan dai ya dage sai mutumen yayi fitsarin a bayansa, aikuwa sai ya saki fitsari shaaaa. To dama kun san mafarkine yake yi, yana tashi sai yaga duk ya jike shinfidarsa. To kun ga shaidan ko abokinsa baya ragama.

KAMMALAWA, DAGA MAI TSOKACI.

Ina fatar za’a amfana kamar yadda muma muka karu bayan nasihar. Allah ya saka ma Malan da alherinsa da wadanda suka gayyato shi da wadanda suka taimaka ga gabatarwarsa da rubuta wannan tsokaci. Da fatar idan an karanta za’a aje a dinga dubawa akai akai domin karatu sai da haka,domin zai yiwu wani abun ba zaka lura dashi ba sai an zo maimaitawa.





No comments:

Post a Comment